Categories
Uncategorized

YADDA ZAKA NEMI TALLAFIN BASHIN KUDI DAGA GOMNATI

Na fahimci mutane da yawa basu fahimci wannan damar ba, shiyasa nace yau dai bari nayi bayani sosai domin ‘yan uwan mu talakawa su gane kuma su amfana, amma kafin nan bari nayi wata matashiya, sau dayawa zaka ji ance shugaba Buhari ya amince a fitar da kudi domin tallafawa masu sana’o’i da ‘yan kasuwa, da masu son su fara Kasuwanci ko harkar kudi, kuma kudaden ana bayar dasu ne a hannun bankuna, amma galibi zaka ga mutanen kudu sun fi na Arewa amfana da abubuwan.

Saboda wasu matsaloli biyu anan Arewa, na farko wakilan gwamnati basu tsayawa su fahimtar da mutane ga manufar shiri kaza, ga amfanin shiri kaza, sai na biyu kuma a nan Arewa muna da wata mummunan ‘dabi’a idan muna adawa da wani shugaba toh mukan yanke tsammani ne daga gare shi gaba daya, kuma ba zamu taba yarda mu nutsu mu gane wani shiri ko tsarin da ya fito dashi ba.

Idan mutum yace baya ra’ayin Buhari to ba zai taba yarda ace ya amfana da Buhari ba, shi dai a barshi da jin haushin Buhari yafi masa amfani a wurin sa, shiyasa bamu amfana da tsare tsaren gwamnati sosai.

Abinda nake so nayi magana akai shine “SMEDAN”, abinda ake nufi da SMEDAN shine “Small and Medium Enterprise Development Agency of Nigeria”.

Wannan cibiya ce ta gwamnatin tarayya wanda aikin ta shine ta tattara bayanin duk wanda yake Kasuwanci a Nigeria, komin kankantar kasuwancin da yake yi, ko Dabinon Naira 200 kake sayarwa ya dace kayi rijistan da hukumar SMEDAN, abu ne mai sauki zan yi bayanin yadda zaka yi ko zaki yi, in sha Allah.

dan kayi rijista da SMEDAN, a take zasu baka Identification Number, sai ka rubuta ta a takarda ka ajiye, saboda tana da muhimmanci fiye da kudin Aljihun ka, zaka ga Lambar ta fara da wasu alphabet kamar haka (SUIN………) haka.

Ko Waina ko ‘Kosai mace take yi ta tabbatar tayi rijistan da SMEDAN, ko saka, ko Kiwon kaji, duk abinda sunan sa saye da sayarwa, kaje kayi rijistan da kan ka SMEDAN a wanan link ( www.smedanregister.ng ) .

Idan kayi rijistan ya zamo gwamnati tana sane da kai kenan akan wannan harkan, kuma ana iya tun-tubar ka a koda yaushe akai.

Abinda ake bukata yayin rijista da SMEDAN:
1. Cikakken suna.
2. Lambar wayar ka.
3. Lambar wayar wani naka.
4. Email dinka, da email din wani naka.
5. National ID number naka, da na wani naka.
6. Jihar ka, local government, unguwar ku.
7. Nau’in kasuwa ko sana’ar da kake yi.
Da sauran su.
8. Sunan da ka saka ko ka rad’a ma sana’ar ka.

Amfanin rijista da SMEDAN:
Idan kayi rijistan zai baka damar samun tallafin kudi kai tsaye daga gwamnatin tarayya, data jihohi har ma da kananan hukumomi, idan kayi rijista da SMEDAN zaka samu damar yin kwasa-kwasai na training akan duk harkokin Kasuwanci da gwamnati take shiryawa.
Sannan zai baka damar karban bashin kudi daga bankuna da sauran cibiyoyin bayar da bashi ko lamunin kudi (Financial Institutions).

Idan kaje karban bashin kudi a banki, to wata cibiya a Online ko ba Online ba, domin Kasuwancin ka, zasu tambaye ka ina lambar ka ta SMEDAN? wato “SMEDAN ID Number”, idan baka da ita ba zasu baka kudin da kake nema ba….

Misali, a yanzu haka gwamnatin tarayya ta fito da hanyoyin karban rancen kudi kala-kala, Musulmi sun yi korafin kudin ruwa (Riba) ko “Interest” an karbi korafin, dan haka yanzu ana iya samun rance wanda ba riba aciki.

bu na karshe…….
Akwai tsare tsare da yanzu haka ana iya samun rancen kudi, sai dai galibin su zaka ga akwai ruwa, kamar
http://cip.smedan.gov.ng/loan/32
Idan ka cika zasu baka.
Nan gaba kadan zamu kawo link din da za’a samu rance wanda babu ruwa aciki in sha Allah.

Daga ‘karshe mu rika yin hakuri kada adawa tasa mu zama wasu irin mutane, koda bamu son shugaban gwamnatin mu rika tsayawa muna fahimtar abinda suke kawowa, kaga wannan SMEDAN din an bude shi tun watan uku, amma galibi mutanen mu basu ma san dashi ba.
Wasu kuma sun gani sun karyata saboda adawa, amma abu ne mai amfani na zahiri.

Categories
Uncategorized

Yadda za ku samu tallafin matasa na N75bn

Gwamnatin Najeriya ta buɗe sabon shafin da matasa za su gabatar da ɓukatarsu ta neman tallafin kuɗi naira biliyan 75 na shirin raya matasa (NYIF) musamman masu neman tallafin bunƙasa kasuwancinsu.

Babban Bankin Najeriya ne ya ɗauki nauyin shirin na ma’aikatar ci gaban matasa da wasanni da nufin saka jari ga matasa masu tunanin kasuwanci a ƙasar domin bunƙasa tattalin arziƙi da kuma samar musu da ayyukan yi.

Ga abubuwa uku da suka kamata ku sani game da tallafin da kuma yadda za ku tura buƙatarku:

  • 1. Wa ya cancanta?

A bayanan da gwamnati ta fitar ta ce sai ƴan tsakanin shekara 18 zuwa 35 da suke da tunani na kasuwanci kuma suke buƙatar tallafin kuɗi ne za su iya neman wannan tallafi.

  • 2. Me ya sa gwamnati ta ƙaddamar da tallafin?

Tallafin kuɗin ya shafi zuba jari ga tunanin matasa na kasuwanci da basirar da suke da ita. Gwamnati ta yi imanin cewa za ta sauya tunanin matasan su koma dogaro da kansu ta yadda za su taimaka wa ci gaban ƙasa. Shirin na tsawon shekara uku ne.

  •  Ta yaya za ka samu tallafin?

Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan kafofin sadarwa na intanet, Lauretta Onochie, ta bayyana cewa matasan da ke son tura buƙatarsu za su shiga wannan shafin,

A danna wannan bulun rubutu https://nyif.nmfb.com.ng/Applicants/New

Amma kafin cike fom ɗin tura buƙata, dole sai mutum ya tabbata yana da lambobin banki na BVN.

Gwamnati za ta saki naira biliyan 25 duk shekara har shekara uku da za a kammala shirin.

Ministan matasa da wasanni Sunday Dare, ya ce matasa 500,000 za su amfana da shirin duk shekara tsakanin 2020 zuwa 2023.

Kuma ya ce shirin na gwamnatin Buhari domin magance matsalar rashin ayyukan yi ga matasa, shiri ne mai ɗorewa.

Categories
Uncategorized

FG ta fitar da adireshin yanar gizo na samun tallafin matasan Kasar

FG ta fitar da adireshin yanar gizo na samun tallafin matasan Kasar

wamnatin tarayya na kokarin dagewa wurin tallafawa matasa da jari musamman masu kananan sana’o’i don rage rashin aikin yi a Najeriya

Hidimar shugaban kasa ta musamman, Lauretta Onochie ta sanar da hakan a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter

Inda tace gwamnatin tarayya ta saki adireshin yanar gizo wadda matasan da basu wuce shekaru 18 zuwa 35 ba zasu bi su samu tallafin

Gwamnatin tarayya na kokarin rage rashin aikin yi a Najeriya, inda ta bayar da adireshin yanar gizo da matasa zasu samu damar samun jari, don tallafawa masu kananan sana’o’i.

Hadimar shugaba Buhari, Laureta Onochie ta sanar da hakan a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba ta kafar sada zumuntar zamani.

Dama ministan matasa da bunkasa wasanni, Sunday Dare, ya sanar da amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari da bayar da naira biliyan 75 don tallafawa matasa.

Categories
Uncategorized

Ma’aikatan NIMC Sun Shiga Yajin Aiki

Ayayin da ’yan Najeriya ke rige-rigen yin rajistar katin shaidar dan kasa, ma’aikatan Hukumar NIMC mai kula da yin rajistsar sun tsunduma yajin aiki.

Ma’aikatan na NIMC sun fara yajin aikin ne a safiyar ranar Alhamis, yayin da wa’adin da Gwamnatin Tarayya ta bayar na rufe layukan wayan da ba a yi musu rajista da lambar dan kasa (NIN) ba ke kara matsowa.

Kungiyar ma’aikatan ta ce, “Kwamitin Zartarwa Reshen NIMCI na umartar ma’aikata daga mataki na 12 zuwa kasa a Hedikwata da rasssan Jihohi da su yi zamansu a gida daga yau 7 ga Janairu 2021, kar su yi aikin komai.

“Muna kuma shawarta mutane da su kaurace wa ofisoshin NIMC na kananan hukumomi da sauran cibiyoyi domin jami’an kwamitin aiki da cikawa za su zaga domin tabbatar da wannan umarni,” inji sanarwar da Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnati (ASCSN) Reshen NIMC, Asekokhai Lucky Michael da Sakatarensa, Odia Victor suka fitar.

Ma’aikatan sun dauki matakin ne domin tabbatar biyan bukatunsu da suka hada da kariyarsu daga cutar COVID-19 da kuma biyan su sabon albashi.

Da alama dai yajin aikin zai kawo cikas ga umarnin Gwamnati cewa kowan dan Najeriya ya yi rajisatar lambarsa NIN, ya kuma hada da lambar layin wayarsa.

Madoga: Daily Trust

Categories
Uncategorized

Jaruma Mai Kayan Mata Ta Siyawa Zpeeety Danƙareriyar Mota Ta Kere Sa’a

A yammacin jiya ne zulaihat Ibrahim wanda ankafi sani da zpeeety ta wallafa a shafinta na Instagram 

inda take Matukar jin dadi inda take cewa.

Banida bakin magana akan wannan abu da jaruma tayi wanda idan tayi abu kamar bazai zamo gaske ba, jaruma kamar wata baiwar Allah ce mai sihiri ,wanda tana da saukin kai bata da matsala sai tana da wuyar ganewa.

Ta kara da cewa ina masoya ina son ku tayi murna kuma ku isar min da godiya ga jaruma wanda ta zamo yanzu daya daga cikin duniya ta.

Ga dai rubutun da ta wallafa sai a gafarcemu da yadda munka fasa abun iya fahimtar mu.

Categories
Uncategorized

Jawabin Mai Martaba Sarkin Kano Akan Shigar Malamai Siyasa

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi II Yayi Bayani Mai Muhimmanci.Ba’a Hana Mutum Ra’ayi Ba, Kowa Yana da Ra’ayinsa, Amman Kada Ku Shigar Da Kanku Cikin Siyasa.

Malamai Su Hau Kan Mumbari ko Hakimai su Tara Jama’a Ace A Zabi Wanannan Jam’iyya Ko Waccan Ba Aikinmu Bane.Ka Futo Akan Mumbari Ko Gidan Radio Ko Gidan Talabijin Shi Ne Ya Kawo Malamai Suna magana ‘yan siyasa suna Magana, Martabar Da Allah Yayi Muku Na Malamai Da Sarautar Nan Kada Mu Ringa Shigar Da Ita Inda Wani Zai Zage mu, Koya Shiga Cikin Mutuncinku Wannan fagen su ne.

Kwanakin Can Baya Munyi Magana Mukace In Za’a Zabi Shugabanni A Zabi Mai Ilimi, ‘Yan Jarida Sukace Sarkin Kano Yace Kar A Zabi Wani Dan Takara Don Bashi Da Certificate, Ni Ban San Maganar Certificate Ba Kuma Maganar Ilimi Nayi.Sannan Mai Martaba Sarki Ya Ja Hankalin ‘Yan Siyasa Dangane da Haifar Da Sara Da Suka A Yayin Kamfen, Da Kuma Munanan Kalamai Da ‘Yan Siyasa Keyi, Indai Sarkin Yace Wannan Ba Komai Bane Sai Warware Addu’o’in Zaman Lafiya Da Sarkin Ke Jagoranta.Sannan Ya Nemi Da A Gurfanar Da Duk ‘Yan Siyasar Da Sukayi Kira Kan A Zubda Jinin Al’umma A Gaban Hukuma. A Karshe Mai Martaba Sarkin Yayi Jan Hankali Sosai Dangane Da Wannan Zabe Dake Karatomu. Ubangiji Allah Ya Karawa Sarki Ingantacciyar Lafiya Da Nisan Kwana Mai Amfani. Ameen.

Categories
Uncategorized

Ronaldo Ya Warke, Zai Buga Wasan Juventus Da Ajax

Rahotanni na nuna cewa tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Robaldo ya warke daga ciwon da ya ji kuma zai samu buga wasan Juve din da Ajax.

Marca ya ruwaito cewa Ronaldo yanzu ya warware kuma zai iya buga wasan da Juve zata yi da Ajax na gasar cin kofin Champions League, sakamakon gwajin da akawa Ronaldo dai da farko ya nuna cewa yana fama da mummunan ciwo da zai sa bazai buga duka wasannin da Juven zata buga da Ajax ba amma yanzu gashi an samu sabon rahoto.

Juventus dai na da wasa da AC Milan amma ga dukkan alamu Ronaldon bazai buga wasan ba dan gudun kada ya sake samun wani ciwon, za’a ajiyeshi sai wasansu da Ajax

Categories
Uncategorized

Ban Yi Ridda Ba Cin Mutuncine Kawai>>Buba Galadima Ya Kare Kanshi

Tsohon na hannun damar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, watau Buba Galadima wanda a yanzu ya koma bangaren adawa yake kuma caccakar gwamnatin APC ta shugaba Buhari ya fito ya kare kanshi akan wani labari dake yawo a shafukan sada zumunta inda yace an zargeshi da yin ridda.Buba Galadima a cikin wani sako da ya fitar ta dandalinshi na sada zumunta yace an rika yada cewa yayi ridda wanda shi kuma maganar da yayi ya danganta zabe da Allah ai Allah ne karshe a wajan gaskiya shiyasa ya fadi haka:Buba yace ga gaskiyar abinda ya fadi anan kasa amma aka samu wasu yara da suka raina manya ana biyansu kudi suna ci musu mutunci:Cewa nayi a hira ta da @voahausa idan Ubangiji ne zai ‘kirga ‘kuri’a babu yadda Buhari zai iya cin zabe, amma wasu mutane sun je sun sauya abinda na fada saboda tsabar rashin son gaskiya. pic.twitter.com/nNvQzUZ8dQ

— Buba Galadima (@buba_galadima) February 17, 2019


Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya mayarwa da Buba Galadiman cewa har yanzu dai ana nan dan kwata-kwata be kamata yayi misalin da Allah ba:

Categories
Uncategorized

Buhari Ya Ce Ba Zai Fadi Zabe Ba

Ku latsa alamar lasifika domin sauraren muryar Shugaba BuhariShugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babu makawa shi ne zai lashe zaben shugaban kasar.Da yake amsa tambayar wakilin BBC kan ko zai amince idan ya sha kaye, sai ya ce “ni zan ci zabe.”Shugaba Buhari ya kada kuri’arsa ce a birnin Daura da ke jihar Katsina tare ds mai dakinsa Aisha Buhari da rakiyar wasu jami’an gwamnatinsa.Sai dai abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce a matsayinsa na mai kare mulkin dimokradiyya zai yi biyayya ga sakamakon zaben kasar.Wasu hotuna sun nuna yadda Shugaba Buhari ya kada kuri’a inda ya zabi kansa.Mai daukar hoto na kamfanin dillancin labaran Reuters ya dauki hotunan takardun kada kuri’ar Buhari, wadanda suka nuna cewa ya zabi kansa.

Buhari

Hukumar zaben Najeriya dai tana ba da shawara kada masu kada kuri’a su bayyana wanda suka zaba, saboda hakan ya saba tsarin tarbiyyar dimokradiyya.

Hare-hare

Sa’o’i biyu kafin bude rumfunan zabe ranar Asabar, al’ummar Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar sun ce sun ji fashewar bama-bamai da harbe-harben bindiga.A wata sanarwa, ‘yan sandan jihar sun ce babu wata barazana ga jama’a. “Jami’an tsaro ne suka yi harbe-harben domin tauna tsakuwa,” in ji sanarwar.Jihar Borno dai ta kasance cibiyar mayakan Boko Haram wadda ta yi shirin ganin ba a gudanar da zaben ba.Kamfanin dillanci labarai na Reuters ya rawaito cewa wasu da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar ne sun kai hari garin Geidam, inda suka tilasta wa jama’ar garin ficewa daga garin.

Me ya sa aka dage zabe?

Sa’o’i biyar kafin bude rumfunan zabe ne dai a ranar Asabar ta 16 ga Fabrairu hukumar zaben Najeria ta sanar da dage zaben.Hukumar ta bayar da dalilan da suka janyo dage zaben da suka hada da yunkurin yin magudi da rashin kai kayan aiki mazabu da kuma rashin kyawun yanayi.Yanzu hukumar ta INEC ta ce ta shirya tsaf domin tafiyar da zaben.

Wannan Layi ne

Yadda zaben yake?

Duk dan takarar da ya samu kuri’un da suka fi yawa, idan dai har ya samu kaso 25 na kuri’un da aka kada a jihohi 24 daga jihohi 36 na kasar.‘Yan takara 73 ne suke neman kujerar shugabancin kasar amma fafatawar ta fi zafi tsakanin ‘yan takarar jam’iyyu biyu.Taken Jam’iyyar shugaba mai ci, Muhammadu Buhari shi ne ‘Next Level’ wato kai Najeriya zuwa matakin ci gaba.Ita kuma jam’iyyar adawa ta PDP wadda tsohon mataimakin shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar yake takara na da taken ‘to get Nigeria working again’, abin da ke nufin jam’iyyar za ta dawo wa najeriyar hayyacinta.Atiku Abubakar ya kalubalanci Shugaba Buhari da lalata shekaru hudun da ya kwashe a kan karaga.Dukkanin ‘yan takarar guda biyu dai sun fito daga yankin arewacin kasar mai yawan musulmai. Kuma dukkanninsu sun wuce shekara 70 da haihuwa.

Matsalolin Najeriya

Najeriya ce dai kasa mafi girma a yawan jama’a da kuma yawan albarkatun man fetur. To sai dai rashawa da cin hanci da kuma gaza zuba rarar da ake samu daga sayar da man a kasuwar duniya ne ke tarnaki ga cigaban kasar.A 2016, kasar ta samu komadar tattalin arziki. An kuma samu jan kafa kafin kasar ta samu ta farfado, al’amarin da ke nuni da cewa ba a samar da isassun ayyukan yi ga miliyoyin matasan kasar da ke neman aiki ba.Za a iya cewa kaso daya bisa hudu na matasan kasar ba su da abun yi.

Wannan Layi ne

Alkaluman masu zabe•Yan takarar shugaban kasa guda 73•Masu katin zabe miliyan 73•Kaso 51 da masu kati ‘yan kasa da shekara 35•Akwai rumfunan zabe dubu 120a fadin kasar.…….

Buhari

Shugaba Buhari ya ce ya murkushe kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, to sai dai har yanzu kungiyar na da karfi.Sannan kuma ana ta yawan samun rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin arewa maso tsakiyar kasar.Najeriya dai ta fuskanci mulkin soji har zuwa 1999, duk da cewa an samu gwamnatocin dimokradiyya wadanda ba su yi tsawon rai ba kafin nan.A bana kasar ke cika shekara 20 da dawo wa turbar dimokradiyya.A 2015 ne aka zabi shugaba Buhari, lokacin da kasar ta kafa tarihi, inda dan takarar jam’iyyar adawa ya kayar da shugaba mai ci.

Categories
Uncategorized

Siyasar Kano: Wankin Hula Ya Kusa Kai Ganduje Dare

Gwamna Ganduje da Abba kabir
Image captionBa a iya bayyana wanda ya lashe zaben na Kano ba har sai da aka shiga zagaye na biyu

Masu iya magana na cewa siyasar Kano sai Kano, kuma a ko da yaushe ta kan zo da wani abu sabo, kamar yadda a bana salon Abba gida-gida da makamantansa suka hadu a yunkurin ‘yan hamayya na kifar da jam’iyyar APC mai mulki.Masu sharhi da dama sun yi hasashen Gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai samu wa’adi na biyu cikin sauki ganin yadda rikici ya dabaibaye jam’iyyar adawa ta PDP da kuma tsagin Kwankwasiyya wadanda su ne manyan masu adawa da gwamnan karkashin jagorancin mutumin da ya gada Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.Amma sai ga wankin hula ya kai APC da Ganduje dare, inda aka tafi zagaye na biyu, kuma PDP ta kasance a gaba da ratar kuri’a 26,655. Kafin daga bisani INEC ta bayyana APC a matsayin waccee ta lashe zagaye na biyun da tazarar kuri’a 8,982 jumulla. Masu sa’ido na gida da waje sun yi Allah-wadai da yadda karashen zaben ya gudana, inda suka ce an yi amfani da ‘yan daba da jami’an tsaro wurin muzgunawa da hana ‘yan adawa kada kuri’a, da kuma aringizon kuri’u, zargin da APC da INEC da ‘yan sanda suka musanta.Sai dai jam’iyyar PDP ta ce za ta bi kadun batun a kotu, kuma masu iya magana na cewa shari’a kamar mace ce mai ciki wadda ba a san me za ta haifa ba sai an gani tukunna, a don haka komai zai iya faruwa.Ko ma dai ya ta kaya a kotun, a zahiri take cewa kawo yanzu Ganduje ya sha da kyar, abin da Hausawa ke cewa ya fi da “kyar aka kamani”. Ga wasu daga cikin abubuwan da suka jawo wa gwamnan matsala a zaben har suka kai ga tasirin Abba K Yusuf da jam’iyyar PDP:

Gandollar

Duk da cewa ya samu kuri’u da dama lokacin da ya lashe zabe a karon farko a 2015, Ganduje ya fara bakin jini a idon wasu ‘yan jihar jim kadan bayan hawansa mulki.Hakan dai ba zai rasa nasaba da rikicin siyasar da ya barke tsakaninsa da mutumin da ya gada Sanata Kwankwaso tun kafin a je ko’ina, da kuma zargin cewa matarsa da aka fi sani da ‘Goggo” tana tasiri matuka a harkokin mulkin jihar.