Categories
Uncategorized

Ban Yi Ridda Ba Cin Mutuncine Kawai>>Buba Galadima Ya Kare Kanshi

Tsohon na hannun damar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, watau Buba Galadima wanda a yanzu ya koma bangaren adawa yake kuma caccakar gwamnatin APC ta shugaba Buhari ya fito ya kare kanshi akan wani labari dake yawo a shafukan sada zumunta inda yace an zargeshi da yin ridda.Buba Galadima a cikin wani sako da ya fitar ta dandalinshi na sada zumunta yace an rika yada cewa yayi ridda wanda shi kuma maganar da yayi ya danganta zabe da Allah ai Allah ne karshe a wajan gaskiya shiyasa ya fadi haka:Buba yace ga gaskiyar abinda ya fadi anan kasa amma aka samu wasu yara da suka raina manya ana biyansu kudi suna ci musu mutunci:Cewa nayi a hira ta da @voahausa idan Ubangiji ne zai ‘kirga ‘kuri’a babu yadda Buhari zai iya cin zabe, amma wasu mutane sun je sun sauya abinda na fada saboda tsabar rashin son gaskiya. pic.twitter.com/nNvQzUZ8dQ

— Buba Galadima (@buba_galadima) February 17, 2019


Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya mayarwa da Buba Galadiman cewa har yanzu dai ana nan dan kwata-kwata be kamata yayi misalin da Allah ba:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *