Categories
Uncategorized

FG ta fitar da adireshin yanar gizo na samun tallafin matasan Kasar

FG ta fitar da adireshin yanar gizo na samun tallafin matasan Kasar

wamnatin tarayya na kokarin dagewa wurin tallafawa matasa da jari musamman masu kananan sana’o’i don rage rashin aikin yi a Najeriya

Hidimar shugaban kasa ta musamman, Lauretta Onochie ta sanar da hakan a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter

Inda tace gwamnatin tarayya ta saki adireshin yanar gizo wadda matasan da basu wuce shekaru 18 zuwa 35 ba zasu bi su samu tallafin

Gwamnatin tarayya na kokarin rage rashin aikin yi a Najeriya, inda ta bayar da adireshin yanar gizo da matasa zasu samu damar samun jari, don tallafawa masu kananan sana’o’i.

Hadimar shugaba Buhari, Laureta Onochie ta sanar da hakan a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba ta kafar sada zumuntar zamani.

Dama ministan matasa da bunkasa wasanni, Sunday Dare, ya sanar da amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari da bayar da naira biliyan 75 don tallafawa matasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *