Categories
Uncategorized

YADDA ZAKA NEMI TALLAFIN BASHIN KUDI DAGA GOMNATI

Na fahimci mutane da yawa basu fahimci wannan damar ba, shiyasa nace yau dai bari nayi bayani sosai domin ‘yan uwan mu talakawa su gane kuma su amfana, amma kafin nan bari nayi wata matashiya, sau dayawa zaka ji ance shugaba Buhari ya amince a fitar da kudi domin tallafawa masu sana’o’i da ‘yan kasuwa, da masu son su fara Kasuwanci ko harkar kudi, kuma kudaden ana bayar dasu ne a hannun bankuna, amma galibi zaka ga mutanen kudu sun fi na Arewa amfana da abubuwan.

Saboda wasu matsaloli biyu anan Arewa, na farko wakilan gwamnati basu tsayawa su fahimtar da mutane ga manufar shiri kaza, ga amfanin shiri kaza, sai na biyu kuma a nan Arewa muna da wata mummunan ‘dabi’a idan muna adawa da wani shugaba toh mukan yanke tsammani ne daga gare shi gaba daya, kuma ba zamu taba yarda mu nutsu mu gane wani shiri ko tsarin da ya fito dashi ba.

Idan mutum yace baya ra’ayin Buhari to ba zai taba yarda ace ya amfana da Buhari ba, shi dai a barshi da jin haushin Buhari yafi masa amfani a wurin sa, shiyasa bamu amfana da tsare tsaren gwamnati sosai.

Abinda nake so nayi magana akai shine “SMEDAN”, abinda ake nufi da SMEDAN shine “Small and Medium Enterprise Development Agency of Nigeria”.

Wannan cibiya ce ta gwamnatin tarayya wanda aikin ta shine ta tattara bayanin duk wanda yake Kasuwanci a Nigeria, komin kankantar kasuwancin da yake yi, ko Dabinon Naira 200 kake sayarwa ya dace kayi rijistan da hukumar SMEDAN, abu ne mai sauki zan yi bayanin yadda zaka yi ko zaki yi, in sha Allah.

dan kayi rijista da SMEDAN, a take zasu baka Identification Number, sai ka rubuta ta a takarda ka ajiye, saboda tana da muhimmanci fiye da kudin Aljihun ka, zaka ga Lambar ta fara da wasu alphabet kamar haka (SUIN………) haka.

Ko Waina ko ‘Kosai mace take yi ta tabbatar tayi rijistan da SMEDAN, ko saka, ko Kiwon kaji, duk abinda sunan sa saye da sayarwa, kaje kayi rijistan da kan ka SMEDAN a wanan link ( www.smedanregister.ng ) .

Idan kayi rijistan ya zamo gwamnati tana sane da kai kenan akan wannan harkan, kuma ana iya tun-tubar ka a koda yaushe akai.

Abinda ake bukata yayin rijista da SMEDAN:
1. Cikakken suna.
2. Lambar wayar ka.
3. Lambar wayar wani naka.
4. Email dinka, da email din wani naka.
5. National ID number naka, da na wani naka.
6. Jihar ka, local government, unguwar ku.
7. Nau’in kasuwa ko sana’ar da kake yi.
Da sauran su.
8. Sunan da ka saka ko ka rad’a ma sana’ar ka.

Amfanin rijista da SMEDAN:
Idan kayi rijistan zai baka damar samun tallafin kudi kai tsaye daga gwamnatin tarayya, data jihohi har ma da kananan hukumomi, idan kayi rijista da SMEDAN zaka samu damar yin kwasa-kwasai na training akan duk harkokin Kasuwanci da gwamnati take shiryawa.
Sannan zai baka damar karban bashin kudi daga bankuna da sauran cibiyoyin bayar da bashi ko lamunin kudi (Financial Institutions).

Idan kaje karban bashin kudi a banki, to wata cibiya a Online ko ba Online ba, domin Kasuwancin ka, zasu tambaye ka ina lambar ka ta SMEDAN? wato “SMEDAN ID Number”, idan baka da ita ba zasu baka kudin da kake nema ba….

Misali, a yanzu haka gwamnatin tarayya ta fito da hanyoyin karban rancen kudi kala-kala, Musulmi sun yi korafin kudin ruwa (Riba) ko “Interest” an karbi korafin, dan haka yanzu ana iya samun rance wanda ba riba aciki.

bu na karshe…….
Akwai tsare tsare da yanzu haka ana iya samun rancen kudi, sai dai galibin su zaka ga akwai ruwa, kamar
http://cip.smedan.gov.ng/loan/32
Idan ka cika zasu baka.
Nan gaba kadan zamu kawo link din da za’a samu rance wanda babu ruwa aciki in sha Allah.

Daga ‘karshe mu rika yin hakuri kada adawa tasa mu zama wasu irin mutane, koda bamu son shugaban gwamnatin mu rika tsayawa muna fahimtar abinda suke kawowa, kaga wannan SMEDAN din an bude shi tun watan uku, amma galibi mutanen mu basu ma san dashi ba.
Wasu kuma sun gani sun karyata saboda adawa, amma abu ne mai amfani na zahiri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *